Friday, December 5
Shadow

Sanata Ali Ndume ya baiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu shawarar rushe kungiyar PENGASSAN

Sanata Ali Ndume ya baiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu shawarar rushe kungiyar manyan ma’aikatan man fetur ta PENGASSAN.

Yace idan kungiyar ta ci gaba da nuna son kai ba tare da la’akari da abubuwan da zasu kawowa al’umma ci gaba ba, ya kamata Gwamnatin tarayya ta soketa.

Ranar Asabat, Kungiyar PENGASSAN ta fara yajin aiki bayan da ta zargi matatar man Dangote da korar membobin ta 800 daga aiki.

A bangaren Dangote, yace Wannan yajin aiki PENGASSAN na son yin amfani dashine dan cimma wani buri nata na saka ‘yan Najeriya cikin wahala.

A hirar da aka yi dashi a Arise TV, Ndume yace baya goyon bayan Ayyukan kungiyoyin kwadago da suke daukar matakan biyan bukatarsu maimakon bukatar al’ummar Najeriya.

Karanta Wannan  Ban yadda da korar da akawa Wike ba, a yi Sulhu zai fi>>Inji Gwamnan Adamawa

Yace ina PENGASSAN take a lokacin da aka cire tallafin man fetur a Najeriya? Sai yanzu ne zasu taso suna magana akan kasuwancin Dangote wanda basu da mallakinshi su ma’aikata ne kawai?

A karshe ya baiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu shawarar soke kungiyar ta PENGASSAN inda yace wasu lokutan sai an dauki tsauraran matakai ake samun sakamakon da ake bukata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *