Friday, January 24
Shadow

Sanata Ali Ndume yayi Allah wadai da kama Hamdiya Sidi saboda kokawa da ta yi da kisan da ‘yan Bìndìgà suke yi a jihar Sokoto

Sanata Ali Ndume yayi Allah wadai da kamawa da kuma hukunta matashiya Hamdiya Sidi, wadda ta fito daga jihar Sokoto ta yi Allah wadai da kisan da ‘yan Bindiga ke yi.

Sanata Ali Ndume yace maganar matashiyar hanyace ta janyo hankalin hukumomi akan abinda ke faruwa a yankin data fito.

Yace sam bai kamata ace an kamata ba.

A sanarwar da kakakin ‘yansandan jihar, Ahmad Rufai ya fitar yace an kama matashiyarne saboda kokarin kawo tarzoma a jihar.

Hakanan wata gamayyar kungiyoyin fafutuka daga Arewa ma sun yi Allah wadai da kamu da aka yiwa matashiyar.

Karanta Wannan  Bidiyo: Tinubu da 'yan majalisa suna rera sabon taken Najeriya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *