Sheikh Ibrahim Ɗahiru Bauchi Ya Jagoranci Tawagar Kungiyar Mu’assasa Domin Yiwa Gwamna Raɗɗa Ta’aziyyar Tsohon Shugaban Ƙasa Buhari.

Tawaga ta musamman daga gidauniyar Shehun Malamin nan Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi, ƙarƙashin jagorancin Sheikh Ibrahim Ɗahiru Usman Bauchi, sun ziyarci Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda PhD,CON, domin yi mashi ta’aziyyar rasuwar Tsohon Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.
Tawagar ƙarƙashin jagorancin ɗan Shehin Malamin Ɗariƙar Tijjaniyya Khalifa Ibrahim Ɗahiru Bauchi sun ziyarci Gwamnan ne a gidan gwamnatin jihar Katsina a yau Lahadi 20 ga watan Yuli 2025.
Da yake gabatar da jawabin dalilin ziyarar ta su Khalifa Ibrahim Ɗahiru Bauchi, ya bayyana sun zo ne a madadin mahaifin nasu domin yiwa iyalai, Gwamnan, da kuma a al’ummar jihar Katsina ta’aziyyar rasuwar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.
Ya cigaba da cewa Marigayin aminin mahaifin su ne da jimawa inda suka shafe shekaru suna a tare musamman a lokacin da lMalam yake gabatar da karatuttukan shi a Kaduna.
Ya bayyana ƙasar nan tayi babban rashin da samun wanda zai maye gurbin shi abu ne mai wahalar gaske, sai dai muyi mashi fatan Allah SWT ya jikan shi da rahama ya kuma bamu haƙurin rashi.
Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda PhD,CON, ya bayyana godiyar shi bisa wannan ziyara mai matuƙar tarihi ya kuma bayyana irin yadda kowa ke kyautata ma Marigayin zato.
Ya ƙara da cewa ko maƙiyin Marigayin ya san cewa mutum ne mai gaskiya kuma adali wanda kowa ke kwaɗayin irin kyawawan halayen shi, “kuma ina kyautata zaton yana aljanna” inji Gwamnan
A cikin irin kyawawan halayen shi a lokacin da ina shugabantar hukumar Smedan yana bamu kasafin kuɗin mu na shekara ɗari bisa ɗari domin kawo cigaba abu ne kuma da mu dai anan Najeriya bamu saba ganin shi ba..
“Sai dai muyi addu’ar Allah SWT ya jikan shi da rahama” Inji Gwamnan
Kwamishinan addinai Isiya Dabai, da mai taimaka ma gwamnan akan makarantun tsangaya ne suka jagoranci tawagar wadda ta ƙunshi wasu daga cikin ƴaƴan Shehun Malamin da kuma wasu manyan Malaman Ɗariƙar Tijjaniyya na jihar Katsina.
Daga: Malam Abdul Maje