Wednesday, May 28
Shadow

Shugaba Buhari ya fadi dalilin da yasa bai halarci babban taron APC ba

Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana dalili da yasa bai samu halattar taron masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar APC ba.

Da yake magana ta bakin kakakinsa, Malam Garba Shehu, Tsohon shugaban yace takardar gayyatar da aka aika masa an aikata ne a makare shiyasa bai samu zuwa ba.

Yace an aikawa Buhari da takardar ranar Litinin amma bata sameshi ba sai ranar Talata, Garba yace ko da jirgin Jet Buhari gareshi ba zai iya halartar taron ba.

Saidai yace duk da rashin halartar taron, Shugaba na baiwa Gwamnatinsa goyon bayan da ya kamata.

Karanta Wannan  Fastocin yakin neman zaben shugaban kasa na 2027 na gwamna Bala Muhammad sun cika Titunan Bauchi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *