Shugaba Tinubu Bai Sauke Ministocin Tsaron Nijeriya Ba – In ji Fadar Shugaban Ƙasa

Mai magana da yawun shugaban kasar Bayo Onanuga ya ce masu yada irin wannan labarin na bogi, masu laifi ne da ya kamata a hukunta su ba tare da bata lokaci ba
Wata kafar yada labarai ta zamani Phoenix browser ce dai ta fitar da labarin inda ta ce Shugaba Tinubu ya sallami minsitocin tsaro da kuma ministan lantarki