
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya aika da wakilai daga Najeriya zuwa kasar Ingila inda suka kaiwa Sanata Ike Ekweremadu dake tsare a gidan yari ziyara.
Wakilan da Shugaba Tinubu ya aika sune Yusuf Maitama Tuggar da Lateef Olasunkanmi Fagbemi da sauransu.
Jakadan Najeriya a Landan, Mohammed Maidugu ne ya karbi tawagar ta Gwamnati.