
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya amince da kudirin dokoki 2 na kafa makarantar nakasassu da kuma asibitin kashi a jihar Gombe.
Majalisar Dattijai ta jinjinawa shugaban kasan kan wannan yunkuri wanda tace zai habbaka harkar ilimi da kiwon lafiya.
Kakakin majalisar Dattijai, Sanata Godswill Akpabio ne ya bayyana haka a yayin zaman majalisar Dattijai na ranar Laraba.
Za’a gina makarantar nakasassun ne a karamar hukumar Dukku dake jihar.