Friday, December 26
Shadow

Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin sake rage farashin kayan abinci

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya sake bayar da umarnin a sake rage farashin kayan abinci.

Shugaban ya bayar da wannan umarnin ne ga majalisar zartaswa, kamar yanda karamin Ministan noma, Senator Aliyu Sabi Abdullahi ya bayyanawa manema labarai a Abuja.

Ministan da yake magana ranar Laraba ya ce shugaban kasar yace a samar da yanda za’a rika safarar kayan abincin a Najeriya ta hanyar sauki ta yanda farashinsa zai sake sauka.

Hakan na zuwane a yayin da wasu manoma ke kukan cewa faduwar farashin kayan abinci na sa su tafka Asara.

Karanta Wannan  Da Duminsa: An kama karin sojoji 26 bisa zarginsu da hannu a yunkurin yiwa shugaba Tinubu Jhuyin mulki

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *