Friday, December 5
Shadow

Shugaban FRSC ya koka kan rashin ɗa’a da cin hanci a tsakanin jami’an hukumar

Shugaban FRSC ya koka kan rashin ɗa’a da cin hanci a tsakanin jami’an hukumar.

Shugaban Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC), Shehu Mohammed, ya bayyana damuwa kan ƙaruwar rashin ɗa’a da cin hanci da shan miyagun ƙwayoyi daga wasu jami’an hukumar, yana mai gargadin cewa hakan na iya lalata amincewar jama’a da mutuncin hukumar.

A yayin taron tsakiyar shekara da aka gudanar a Abuja, Mohammed ya umurci manyan jami’ai da su dauki matakai kan wadannan kalubale tare da tabbatar da ladabtarwa da gaskiya a tsakanin ma’aikata. Ya ce hukumar za ta ladabtar da wadanda suka sabawa ka’idoji tare da yabawa masu bin doka domin karfafa gwiwa.

Karanta Wannan  Ɗan Tsohon Shugaban Kasa, Malam Umaru Musa Yar'adua, Musa Umaru Musa Yar'adua Ya Ziyarci Tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo A Gonarsa Dake Otta Jihar Ogun

Shugaban FRSC ya bayyana cewa gwamnati ta amince da gyaran dokar hukumar da zai sauya sunanta zuwa Nigeria Road Safety Commission, tare da fadada aikinta zuwa dukkan titunan jama’a da kafa rundunar musamman.

Duk da kalubalen ciki, Najeriya ta samu lambar yabo ta Kofi Annan Road Safety Award a matsayin kasa mafi kyau a harkar kiyaye hadurra a Afrika. Hakanan hukumar ta kara daukar matakan wayar da kan jama’a da amfani da fasahar zamani domin inganta ayyukanta.

Mohammed ya yi kira da karin hadin kai tsakanin jami’an hukumar da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da ingantaccen aiki da rage hadurran mota a fadin kasar.

Karanta Wannan  Dan Gidan Attajiri Dahiru Mangal, Zai Auri 'Yar Sanata Kwankwaso

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *