Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya daga zaman majalisar zartaswa saboda mutuwar shugaban sojojin Najeriya Lt General Taoreed Lagbaja.
Shugaban yace za’a sanar da sabuwar ranar yin zaman nan gaba.
A yau, Larabane ya kamata a yi zaman na majalisar zartaswar amma aka dagashi sai abinda hali yayi saboda girmama shugaban sojojin da ya mutu.
Shugaban ya kuma bayar da umarnin yin kasa-kasa sa tutocin Najeriya har nan da sati daya.