Monday, January 6
Shadow

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya fara bin manyan Arewa yan rokon su amince da kudirin Haraji da yake son aiwatarwa

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya fara aika wakilai ga manyan mutane a Arewa dan ya jawo hankalinsu su amince da sabon kudirin dokar canja fasalin Haraji da yake son aiwatarwa.

Rahotanni daga fadar shugaban kasa, Kamar yanda jaridar Punchng ta samo sun ce shugaban yana aikawa mutane daidaiku da kungiyoyi wakilai dan jawo hankalinsu su amince da kudirin dokar tasa.

Hakan na zuwane a yayin da gwamnonin Arewa suka ki baiwa shugaban kasar hadin kai game da sabuwar dokar harajin.

Sabuwar dokar Harajin dai ana ganin zata fi amfanar jihohin kudu wadanda suka fi kawo kudin shiga inda ake maganar jihar data fi kawo kudin shiga itace zata samu kudi masu yawa.

Karanta Wannan  Akalla mutum 1,301 ne suka mutu a yayin aikin Hajjin bana – Saudi Arabia

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *