Friday, December 5
Shadow

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya jinjinawa Hilda Baci wadda ta dafa shinkafa a Tukunya mafi girma a Duniya

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya jinjinawa Hilda Baci wadda ta dafa shinkafa a Tukunya mafi girma a Duniya.

Shugaban kasar yayi wannan jinjinane ta bakin ministan yada labarai, Mohammed Idris, inda yace abinda Hilda ta yi ya jawowa Najeriya suna a Idon Duniya kuma yace ‘yan kasa na al’fahari da ita.

Shugaban yace, matasa su yi koyi da irin abinda Hilda ta yi inda ya sha alwashin cewa gwamnati zata tallafawa irin wannan kokari nan gaba.

Hilda Baci dai ta yi wannan abu ne dan shiga kundin Tarihin Duniya hakanan a shekarar 2023 ma ta yi girki na lokaci mafi tsawo a Duniya.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo Gwanin ban Tausai: Yanda Mijina ya hanani zuwa jana'izar babana bayan ya ràsù, inji wannan matar

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *