
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya yafewa wasu masu manyan laifuka su 17 dake tsare a gidajen yarin Najeriya daban-daban.
Daga ciki akwai tsohon dan majalisar tarayya, Sanata Farouk Lawal, da Marigayi janar Mamman Jiya Vatsa, da Herbert Macaulay.
Cikin wadanda shugaban ya yafewa badda wanda aka kama da laifin safarar miyagun Kwayoyi.
Me magana da yawun shugaban kasar, Bayo Onanuga ne ya bayyana haka inda yace shugaba Tinubu ya yi wannan yafiyar ne bayan zaman majalisar Iyayen kasa a ranar Alhamis a Abuja.
Akwai kuma masu laifi 65 da shugaba Tinubu ya ragewa yawan shekarun da zasu yi a gidan yarin.
Akwai kuma masu laifi guda 7 da shugaban ya ragewa hukunci daga hukuncin kisa zuwa Hukuncin daurin rai da rai