
Shugaban Kwamitin Da’a na majalisar Dattijai, Senator Neda Imasuen, wanda ya fito daga jihar Edo zai bar jam’iyyarsa ta Labour party zuwa jam’iyyar APC.
Rahotanni ya shirya tsaf dan canja jam’iyyar tasa.
Ya bayyana cewa, zai dauki wannan mataki ne saboda jam’iyyarsa ta Labour party ta rasa Alkibla.
Yace kuma zai sanar da komawarsa jam’iyyar APC ranar 12 ga watan Yuni a birnin Benin City.