Wednesday, January 15
Shadow

Shugabannin ƙwadago da na gwamnati na tattaunawa

Wakilan ƙungiyar ƙwadago ta NLC da TUC na can na ci gaba da tattaunawa da wakilan gwamnati a ofishin sakataren gwamnati da ke Abuja.

Wannan dai na zuwa ne bayan kwashe sa’o’i da dama gamayyar ƙungiyoyin ƙwadago suna yajin aiki a Najeriyar, inda asibitoci da makarantu da sauran ma’aikatu suka kasance a rufe.

Gwamnatin shugaba Tinubu ta nemi ‘yan ƙungiyar da su janye yajin aikin su koma bakin tattaunawa.

Wannan tattaunawar ita ce zangon farko kafin wadda za a yi a ranar Talata.

Karanta Wannan  Muna Maraba da Kwankwaso ya zama mataimakin Obi>>Inji Jam'iyyar Labour party

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *