Friday, December 5
Shadow

Sojoji Sun Kàshè Manyan masu ikirarin Jìhàdì A jihar Bòrnò

{“remix_data”:[],”remix_entry_point”:”challenges”,”source_tags”:[],”origin”:”unknown”,”total_draw_time”:0,”total_draw_actions”:0,”layers_used”:0,”brushes_used”:0,”photos_added”:0,”total_editor_actions”:{},”tools_used”:{},”is_sticker”:false,”edited_since_last_sticker_save”:false,”containsFTESticker”:false}

A ranar Litinin, 9 ga watan Yuni 2025, dakarun haɗin gwiwa na sojoji sun kai farmaki maɓoyar ƴan ta’adda na Boko Haram da ISWAP a Nzalgana da ke ƙaramar hukumar Gujba da kuma yankin Timbuktu Triangle.

Sanarwar da rundunar ta fitar a shafinta na X ta ce an kashe ƴan ta’adda da dama ciki har da jagororinsu.

Daga cikin waɗanda aka kashe akwai Ameer Malam Jidda, wani babban kwamanda da ke da tasiri a ƙauyukan Ngorgore da Malumti.

Sojojin sun ƙara cewa sun kuma ƙwato makamai da wasu abubuwa masu muhimmanci a wani farmaki daban da suka kai Malamfatori.

A ‘yan kwanakin nan, hare-haren Boko Haram da ISWAP sun ƙaru, inda a watan da ya gabata ƙungiyar ta kai hari da jirgi mara matuƙi a garin Marte da ke Jihar Borno.

Karanta Wannan  Wasu Daga Cikin Falalar Goman Farko Na Watan Zulhijja

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *