
Darajar Nair ta farfado a kasuwar canji inda a jiya aka sayi dalar Amurka akan Naira 1,493.
A bayanan da CBN ya saki, an ga cewa farashin Dala ya sakko daga Naira 1,506 kamar yanda aka siya a ranar Laraba zuwa Naira 1493 kamar yanda aka siya a ranar Alhamis.
Hakan na nuna an samu saukin Naira 13 kenan.