
Rahotanni sun bayyana cewa, sojojin Najeriya guda 11 da kasar Burkina Faso ta saki tare da jirginsu C-130 sun isa kasar Ghana
Rahoton yace sun samu tarba me kyau a kasar wanda hakan ke kara tabbatar da kyakkyawar alakar dake tsakanin Najeriya da kasar Ghana.
Hakanan kuma a ranar Asabar ne zasu ci gaba da tafiyarsu zuwa kasar Portugal wadda dama can suka nufa suka makale a kasar Burkina Faso.