Monday, April 21
Shadow

Sojojin Najeriya sun kashe ƴanbindiga uku a Taraba

Sojojin Najeriya masu aiki na musamman na Operation WHIRL STROKE (OPWS) sun sanar da kashe ƴanbindiga uku, sannan suka lalata mazauninsu tare da ƙwace makamai a ƙaramar hukumar Karim Lamido da ke jihar Taraba.

Sojojin sun samu nasarar ce a ranar 5 ga Afrilu, kamar yadda kakakin sashen Olubodunde Oni ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar.

Sanarwar ta ƙara da cewa da sojojin suka isa yankin Chibi, sai ƴanbindigar suka fara tserewa, “inda sojojin suka bi sahunsu suka yi musayar wuta, inda dakarunmu suka kashe ƴanbindigar guda uku, sannan suka tarwatsa mazauninsu, tare da ƙwato makamai.”

Sanarwar ta ƙara da cewa sojojin na Najeriya sun yi sintiri a yankin Dutsen Zaki da Achalle a kwanakin baya, inda suka tarwatsa mazaunan ƴanbindiga da dama.

Karanta Wannan  Ashe shima Godswill Akpabio ya taba sukar Bukola Saraki bayan da ya canja mai kujerar zama kamar yanda a yanzu fadanshi da Sanata Natasha Akpoti ya samo Asali ne daga canja mata kujera

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *