Monday, December 16
Shadow

Sojojin Najeriya sun kashe ‘yan bindiga biyar tare ƙwato makamai a Kaduna

Sojojin Najeriya da ke aiki da rundunar ‘Operation Whirl Punch’ mai yaƙi da masu garkuwa da mutane sun kashe ‘yan bindiga biyar a yankin Dantarau da ke ƙaramar hukumar Kajuru a jihar Kaduna.

Cikin wata sanarwa da kwamishin tsaro da al’amuran cikin gida na jihar, Samuel Aruwan ya fitar, ya ce dakarun sojin waɗanda ke aiki a yankunan ƙananan hukumomin Kachia da Kajuru sun kuma ƙwato makamai.

”Sojojin sun ƙwato bindiga ƙirar AK-47 guda biyu, da bindiga ƙirar gida guda ɗaya, ƙwason zuba alburushi na Ak-47 guda tara, da harsasai 250 da babura biyu da wayoyin oba-oba biyu”, in ji sanarwar.

Sanarwar ta ƙara da cewa sojojin sun kuma lalata sansanonin ‘yan bindigar a yankin Sabon Birnin Daji da ke ƙaramar hukumar Igabi.

Karanta Wannan  Kalli Hotuna: An kamashi da ma-ka-mai wanda yake shirin sayarwa da 'yan Bindiga

Aruwan ya kuma ce a lokacin samamen sojojin sun yi musayar wuta da ‘yan bindigar lamarin da ya sa wasu da dama daga cikinsu suka tsere da raunukan harbin bindiga

Kan hakan ne Aruwan ya yi kira ga mazauna yankunan ƙaramar hukumar Igabi su sanya idanu kan mutanen da za su gani da raunukan bindiga.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *