
Gwamnatin tarayya tace tafiye-Tafiyen da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ke yi sun kawowa Najeriya zuba jarin dala Biliyan $50.
Ministar masana’antu, Jumoke Oduwole ce ta bayyana hakan a wata ganawa da aka yi da ita ranar Talata a Abuja.
Tace shugaban ya halarci taruka irin su na manyan kasashe mafiya karfin tattalin arzikin a Duniya watau G20 wanda kuma kamfanoni da yawa suka hadu a wajan.
Tace wakilan wadannan kamfanoni da masu zuba jari sun kawo ziyara Najeriya kuma sun ga damar zuba jari kuma sun bayar da tabbacin zasu zo su zuba wannan jari a Najeriya.