
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa, Talauci shine babban makiyin dan Adam.
Ya bayyana hakane a cikin sakonsa na ranar yaki da Talauci ta Duniya.
Yace Talauci na kawo Jahilci, Cutuka, Matsalar tsaro, da rashin Tabbas a rayuwa.
Yace saka wannan rana a matsayin ranar yaki da Talauci ta Duniya kira ne ga gwamnatoci da kungiyoyin fafutuka dama duka masu ruwa da tsaki kan a hada hannu dan yakar Talauci.
Yace dolene a dauki matakan yaki da Talauci a Najeriya.