Sunday, November 16
Shadow

Talauci ne babban makiyin dan Adam>>Inji Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa, Talauci shine babban makiyin dan Adam.

Ya bayyana hakane a cikin sakonsa na ranar yaki da Talauci ta Duniya.

Yace Talauci na kawo Jahilci, Cutuka, Matsalar tsaro, da rashin Tabbas a rayuwa.

Yace saka wannan rana a matsayin ranar yaki da Talauci ta Duniya kira ne ga gwamnatoci da kungiyoyin fafutuka dama duka masu ruwa da tsaki kan a hada hannu dan yakar Talauci.

Yace dolene a dauki matakan yaki da Talauci a Najeriya.

Karanta Wannan  Kwana hudu da suka gabata na musulunta, amma ana gayamin za'a koreni daga wajan aiki na idan ban bar Musulunci ba, Saidai na zabi Allah da Addinin Musulunci maimakon aikin nawa>>Inji Ba'amurke, Martin

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *