Tapswap sun ɗage Ranar da za ta fashe, za su sake sanya Lokaci.
Shahararriyar Manhajar haƙo sulalla ta Tapswap ta hanyar TON Blockchain ta ce ta jinkirta ranar bajakolin kasafin sulalla ga masu amfani da shi zuwa wani lokaci da ba su sanar ba, yayin da ma’aikantan su ke kokarin neman karin hanyoyin da za su inganta shi domin amfanar mutane da yawa.
Shugaban sashen sadarwa na Tapswap John Robbin ne ya bayyana hakan a dandalin sadarwarsa na X ranar Laraba.
Dandalin wanda ke buƙatar masu amfani da shi da su rika danna alamar da ke tsakiyar manhajar Tapswap a Telegram don hakar sulalla a kwanan nan ya samu karbuwa a tsakanin ‘yan Najeriya inda suke duƙufa wajen latsa fuskar wayarsu don neman kudi, kuma ya tara mutane sama da Miliyan 50 tun bayan da aka kaddamar da shi a ranar 15 ga watan Fabrairun shekarar 2024.
A cewarsa, har yanzu ba a tabbatar da hanyar da za su rarraba sulallan ba, yana mai jaddada cewa ba za a iya sanar da hanyoyin ba kafin fashewar Coins ɗin.
An jinkirta ƙaddamar da shi har zuwa 1 ga watan Yuli sannan ma Za a sanar da sabuwar ranar.
Shugaban sadarwa na Manhajar ya kuma lura cewa masu amfani da Dandalin haƙar sulallan, da ke cin zarafin wasan ta hanyar coge, za a yi maganin su ta hanyar da ta dace.
Da yake magana game da ayyukan hakar ma’adinai ya ce “Ku Bude Manhajar kawai sai ku danna shi, Wannan zai ba damar tara sulalla dai-dai da ƙwazon ku idan muka ƙaddamar da shi.
Adadin sulallan da kuke son samu, iya adadin tattaɓawar da za ku yi.
A kan zaɓin ƙara bugun haƙa wanda ya riga ya ƙare, wakilin Manhajar ya ce ba sabon abu ba ne, ya kara da cewa “Mun ɓullo da wata sabuwar hanyar zuba hannun jari domin samun amfanuwa da yawa.
Mun kuma gabatar da wani tsarin x2 saboda sababbin masu shigowa wanda zai taimaka musu su samo rabo mai kyau.
“Wani tsari ne da ya baiwa mutanen da suka shiga kwanan nan damar yin gogayya da mutanen da suka fara tun da farko, amma muna sa ran yin amfani da kuɗin da muka samu daga gare ta don inganta wasan nan gaba.
Ma’aikatan mu 25 na aiki ba dare ba rana don ci gaban Manhajar, Muna son kasancewa cikin yanayi mai kyau na dogon lokaci. “
Ya kuma bukaci mutane da su ci gaba da shiga manhajar, saboda lokaci ya yi da mutane za su samu tagomashi.
Ku tuna cewa ’yan Najeriya da suka hada da matasa da dattijai sun duƙufa latsa wannan Manhajar a wayoyinsu, inda wasu ke ikirarin cewa suna jiran ta fashe domin sayen motoci da gidajen alfarma daga dimbin dukiyar da suka tara.
Daga Lukman Aliyu Iyatawa