Fara Sana’a abu ne me sauki sosai, musamman a wannan zamanin da muke na yanar gizo da kafafen sada zumunta.
A yanzu ba lallai sai kina ko kana da jari ba sannan zaka fara sana’a ba.
Kamin ka fara sana’a, yana da kyau kasan sana’ar kuma kasan ba a dare daya da fara wannan sana’a zaka yi nasara ba, akwai kalibale.
Yana da kyau amma ba lallai bane ya zama kana ko kina son sana’ar da kike, ko kake. Mana’ana, zai iya zama ka tsani sana’a amma tana kawo kudi, kaga kuwa bai kamata kawai dan ka tsaneta ka daina ba.
Ita sana’a yawanci yana da kyau a fara koyanta kamar yanda muka bayyana.
Kuma akwai hanyoyin koyo da yawa, wata kila tana bukatar ka je makaranta irin ta watanni 3 ko watanni shida dinnan wanda ake koya saka, dinki, da sauransu.
Ba lallai sai kin ko ka je irin wadannan makarantun ba, Watakila abokin yayanka ko abokinka ko yayan abokinka, ko abokin babbanka, ko makwabcinku yana wannan sana’a da kake sha’awa, duk zaka iya in amfani da wannan dama wajan koyan wannan sana’a.
Idan Allah ya taimakeka ko ya taimakeki, watakila a cikin wannan koyon da kake ko kike sai ki ga kin samu Jari.
Tana iya yiyuwa sana’ar da kake son yi ko kike son yi jari kawai kike ko kakake bukata, watakila wani tunani ne naka ko naki wanda kike ko kake ganin idan ka samu kudi zaka iya maidashi sa’a mai kawo kudi.
A wannan yanayi idan baka ko baki da kudi akwai hanyoyi da ya kamata ka bi ko kibi dan samun Jari.
Zaki iya tambayar mahaifi ko mahaifiya.
Zaka iya tambayar yaya ko wani dan uwa ya baka jari ka masa bayanin irin sana’ar da kake son yi yanda zai gamsu cewa ba wasa bane.
Idan wannan sana’a tana da kyau sosai kuma ka yadda ko kin yadda da ita, zaki iya gabatar da ita ga wani me kudi ko dan kasuwa dan neman ya zuba jari a gwada.
Akwai Kungiyoyi na gida Najeriya da kasashen waje dake taimakawa mutane masu fasaha ko son fara sana’a amma basu da jari, ka ko ki nemi irin wadannan Kungiyoyi dan su tallafa maka, kumama har gwamnati daga lokaci zuwa Lokaci suma sukan tallafawa matasa masu neman jari da kudi.
Misali a Najeriya akwai Tony Elumelu Foundation kyauta suke bayar da jari me kwari sosai na miliyoyin Naira idan dai sana’a na fda kyau.
Sai kuma Sana’ar da bata bukatar Jari ko a koyeta.
A yayin zamanin kafafen sadarwa, zaka ko zaki iya zama kana ko kina sana’a ba tare da jarin ko sisi ba, kawai data da wayar ka kake bukata.
Kana iya zuwa kowane shago na kayan sayarwa wanda kake da sha’awar yin kasuwancinsu, sai su baka hotunan kayan ka rika sakawa a shafukanka na sada zumunta idan an samu me saye sai kawa shagon magana a aika musu.
Bayan nan, Kana iya bude shafi a Facebook, Tiktok, ko YouTube ka rika koyar da wani abu da ka iya wanda kake ganin zai amfani mutane, idan Allah ya taimeka ka samu daukaka kuma wadannan shafukan suka fara biyanka shikenan ka samu sana’a hakanan kamfanoni da masu kananan sana’o’i ma zasu iya rika baka tallah.