
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour party, Peter Obi ya bayyana cewa, shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ne ke da alhakin rikicin dake faruwa a cikin jam’iyyar su.
Obi ya bayyana hakane a yayin da ake masa tambayoyi a gidan Talabijin na Arise TV inda yace yana da tabbacin Gwamnatin tarayya ce ta dauki nauyin rikicin dake faruwa a jam’iyyar.
Ya bayyana cewa, suna son yada rikici a cikin jam’iyyar ta Labour Party.