Tinubu ya bai wa jihohi naira biliyan 108bn kan ambaliya da zaizayar ƙasa – Shettima.
Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya amince da kuɗi Naira biliyan 108 ga jihohi 36 na ƙasar domin yaƙi da ambaliya da sauran nau’ukan bala’o’i.
Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa a ranar Laraba.
Da yake bayyani a lokacin da ya karɓi baƙuncin Shugaban Majalisar Wakilan Najeriya, Abbas Tajudden, ya bayyana ambaliyar ta Borno a matsayin “bala’i ga ƙasar baki ɗaya.”
“Shugaba ƙasar ya nuna niyyarsa ta haɗa hannu da jihohi domin magance irin waɗannan matsalolin,” inji Shettima.
“Ba a daɗe ba ya amince a ba kowace jiha Naira biliyan uku domin magance irin waɗannan matsalolin,” kamar yadda shafin talabijin na Channels na intanet ya ruwaito.
A nasa ɓangaren, Tajudeen ya jajanta wa Shettima da Tinubu da gwamnati da al’ummar Borno bisa wannan ibtila’in, sannan ya tabbatar da cewa majalisa za ta taimaka wa waɗanda lamarin ya shafa.
“In sha Allah komai zai wuce kuma mutane za su koma garuruwansu, su cigaba da rayuwarsu kamar yadda suka saba kamar babu abun da ya faru. Don Allah ka isar mana da saƙonmu na jaje zuwa ga gwamna da al’ummar Borno,” inji shi.