Wednesday, January 15
Shadow

Tinubu ya ce a kamo maharan da suka kashe mutum 50 a Katsina

Shugaba Tinubu ya umurci jami’an tsaro da su kamo maharan da suka kai hari a ƙananan hukumomin Dutsin-Ma da Kankara na jihar Katsina da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama tare da tabbatar da an hukunta su.

Shugaban ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara na musamman Ajuri Ngelale ya fitar a ranar 11 ga watan Yuni, 2024 yana mai kakkausar suka kan yawaitar hare-hare a ƙasar.

A yayin da ya bayyana sabbin hare-haren a matsayin munanan hare-hare, shugaban ya jaddada cewa za a ƙara ƙaimi wajen tabbatar da tsaron ‘yan kasa da kuma taarwatsa ‘yan ta’adda gaba daya da sauran masu tayar da zaune tsaye da kuma baƙin ciki a kowane ɓangare na ƙasar.

Karanta Wannan  Ya kamata EFCC ta kyale Bobrisky ta koma kan 'yan siyasa>>Inji Peter Obi

Shugaban ya jajantawa iyalan waɗanda abin ya shafa, da gwamnati da kuma al’ummar jihar Katsina, tare da addu’ar Allah ya jikan waɗanda suka rasu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *