Friday, December 5
Shadow

Tinubu ya dawo da zaman lafiya a Arewa-maso-Yamma, inji Gwamnan Kaduna, Uba Sani

Tinubu ya dawo da zaman lafiya a Arewa-maso-Yamma, inji Uba Sani.

Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya ce Shugaba Bola Tinubu ya daidaita harkar tsaro a yankin Arewa maso Yamma tare da farfado da harkokin noma da ‘yan ta’adda suka durkusar da su a baya.

Da yake jawabi a taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC na Arewa maso Yamma da aka gudanar a Kaduna ranar Asabar, Sani ya ce yankin da a da ke zama cibiyar ta’addanci, garkuwa da mutane da kuma ayyukan ‘yan bindiga, yanzu yana samun sauyi mai ma’ana.

“Tun kafin Shugaba Tinubu ya hau mulki a shekarar 2023, yankin Arewa maso Yamma ne cibiyar ta’addanci, garkuwa da mutane da sauran laifukan tashin hankali,” in ji shi.

Karanta Wannan  Kungiyar dake saka ido kan makamin kare dangi ta Duniya tace kasar Ìràn ta munafurceta ta hanyar kin bayyana mata shirin da take na mallakar makamin

“Ba za ka iya yin tafiya daga wuri zuwa wani wuri ba. Manoma ba za su iya zuwa gonakinsu ba. Rayuwa ta kasance mai wahala, kuma cike da tashin hankali. A wani lokaci, al’amura sun kai matsayin da babu fata. Amma bayan shekaru biyu da hawansa mulki, abubuwa sun canza.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *