
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya nuna alhini da jimami da alhini bisa rashe-rashen da suka faru a jihohin Kano da Neja, yana mai bayyana lamarin a matsayin babban rashi ga ƙasa baki ɗaya.
A wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Juma’a, Shugaba Tinubu ya nuna matuƙar kaɗuwa kan hatsarin mota da ya rutsa da ‘yan wasan Jihar Kano a hanyarsu ta dawowa daga gasar wasanni ta ƙasa da aka kammala a Jihar Ogun.
Shugaban Ƙasa ya yi addu’ar Allah ya jikan waɗanda suka rasa rayukansu a cikin hatsarin, ya kuma roƙi Allah ya bai wa iyalansu da daukacin al’ummar Kano haƙuri da juriya.
Ya ce hanya mafi inganci ta girmama su ita ce ɗaukar matakan kariya domin rage aukuwar irin wannan ibtila’i a gaba.
Baya ga haka, Tinubu ya bayyana alhini kan ambaliya mai tsanani da ta afku a ƙaramar hukumar Mokwa da ke Jihar Neja, wacce ta yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama tare da raba daruruwan iyalai da muhallansu.