Friday, December 5
Shadow

Tinubu ya naɗa shugaban PenCom

Tinubu ya naɗa shugaban PenCom

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya naɗa Opeyemi Agbaje, tsohon Mataimakin Babban Manaja (AGM) na bankin GTBank, a matsayin sabon shugaban Hukumar Kula da Fensho ta Ƙasa (PenCom).

Agbaje ya taɓa zama Daraktan Gudanarwa a Metropolitan Bank kafin ya bar harkar banki.

TheCable ta rawaito cewa wannan naɗin ya zo ne bayan wa’adin kwanaki bakwai da Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC) ta bayar, inda ta nemi a gaggauta sake kafa hukumar gudanarwa ta PenCom, tare da yin gargaɗin shiga yajin aiki idan gwamnati ta ƙi bin umarnin.

A wata sanarwa da aka fitar a ranar Litinin, an bayyana shi a matsayin masani mai tasiri a fannoni na kasuwanci, tattalin arziki da manufofin gwamnati.

Karanta Wannan  Kuma Dai: Gwamnatin Tarayya zata sae ciwo bashin Dala $1.75bn

Agbaje ya kammala karatu a Jami’ar Ife (wanda yanzu ake kira Jami’ar Obafemi Awolowo), inda ya yi fice a fannin Shari’a a shekarar 1985, kuma Lauya a 1986.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *