Wednesday, January 15
Shadow

Tinubu zai dawo Najeriya bayan ziyarar da ya kai kasashen China, UAE da Ingila

A yau,Lahadi ne shugaban kasa,Bola Ahmad Tinubu zai dawo gida Najeriya bayan ziyarar da ya kai kasashen China, UAE da Ingila.

Ranar 29 ga watan Augusta ne shugaban ya bar Abuja zuwa Beijing inda ya dan tsahirta a Dubai, UAE.

Ya isa Beijing ranar 1 ga watan Satumba.

Ranar 2 ga watan Satumba ne dai shugaban ya fara ziyarar a aikace inda ya gana da shugaban kasar China Xi Jinping sannan aka masa fareti da harbin bindiga na ban girma.

A taron, Najeriya da kasar China sun sakawa wasu yarjejeniyoyi guda 5 na ci gaban kasashen biyu hannu kamar yanda kakakin shugaban kasar, Bayo Onanuga ya bayyanar.

Karanta Wannan  Tinubu bai faɗi nawa albashi mafi ƙanƙanta zai kasance ba a jawabinsa

Hakanan shugaban kasar na China Xi Jinping da matarsa, Peng Liyuan sun shiryawa shugaba Tinubu wata liyafar dare wadda aka nuna al’adun kasar Chinan.

Daga nan Shugaba Tinubu ya tafi zuwa kasar Ingila Birnin Landan inda ya yi ‘yan kwanaki.

A wasu Rahotannin ma ance ya ga likita a kasar ta ingila.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *