Wednesday, January 14
Shadow

Tonon Silili: Ta fallasa ashe kudi Inyamurai suka bayar aka zuga Trump akan Najeriya

Biyo bayan labarin cewa, Gwamnatin Najeriya ta baiwa wani kamfani a kasar Amurka dala Miliyan 9 su rika gayawa Gwamnatin Amurka irin kokarin da take akan kare Kirista.

Labari ya bayyana cewa ashe tun farko wasu Inyamurai ne suka samu irin wannan Kamfani suka biyasu kusan dala 60,000.

Akan su kaiwa shugaban kasar, korafinsu na cewa ana yiwa Kiristoci Khìsàn Kyìyàshì a Najeriya.

A wani rahoton ma an ce sun nemi Trumo ya taimaka musu su zamu kasar Biafra inda suka wa Amirkar Alkawarin cewa zasu bata damar dibar mai a yankinsu na Biafra idan hakan ta tabbata.

Saidai Gwamnatin Tarayya ta gano wannan shiri inda ita kuma ta samu wani kamfani irin wanda inyamuran suka dauka amma yafi na Inyamuran karfi dan ya wanke ta a wajan Gwamnatin Amurka.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: Ina nan da raina>>Inji Sabuwa Dadin Kowa

Shine Gwamnatin ta baiwa Kamfanin Dala Miliyan 9 dan yayi wannan aiki.

A martaninsa game da wannan Lamari, babban dan jarida kuma tsohon hadimin shugaban kasa, Reuben Abati ya bayyana cewa babu Laifi game da wannan zunzurutun kudade da Gwamnatin tarayya ta ware dan wanke kanta a wajan Gwamnatin Amurka, musamman Lura da yawa kudaden da Inyamuran suka kashe wajan bata mata suna.

Hakanan shi kanshi baturen da Inyamuran suka dauka ya musu aikin kai wannan magana wajan shugaban Amurka ya tabbatar da lamarin.

Karanta Wannan  An kama magidanci da Abokinsa da sukawa Agolarsa fyàdè, suka dirka mata ciki

Inda ya rubuta cewa, yasan kamfanin da Gwamnatin Najeriya ta dauka aiki ya wanke ta a wajan kasar Amurka.

Saidai yace hakan ba zai canja matsayar shugaban Amurkar ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *