
Wannan bidiyon yanda lamarin rikicin rusau ya faru ne a jihar Kano inda Rahoton Daily Trust yace jami’an tsaro sun kashe mutane 4.
Lamarin ya farune a Rimin Auzinawa inda aka rushe gidajen mutane su kuma suka mayar da martani ta hanyar jifar jami’an tsaron.
Su kuma jami’an tsaron sun bude wuta inda hakan yayi sanadiyyar kisan mutane 4.