Kamfanin Guinness mai yin kayan sha ciki har da giya ya sanar da shirinsa na ficewa daga Najeriya saboda matsanancin halin da tattalin arziƙin ƙasar ke ciki.
Kamfanin wanda ya kwashe fiye da shekra 74 yana aiki a Najeriya ya ce zai fice sannan kuma zai sayar da dukkannin hannin jari mallakarsa ga rukunin kamfanoni na Tolaram Group na ƙasar Singapore.
Jaridar People’s Gazette ta rawaito cewa kamfanin na Guinness dai ya yi asarar naira biliyan 61.9 a watan Yulin 2023 da Maris na 2024 bayan hawan Tinubu inda ya rage wa naira daraja.
Guinness Nigeria Plc, kamfani ne wanda yake cikin jerin sunayen kamfanoni da ke hada-hadar hannayen jari a Najeriya kuma an yi masa rijista a kasar a matsayin kamfanin da ke shigar da giya samfirin Stout daga Dublin.