
Gwamnan jihar Kogi Alhaji Ahmed Usman Ododo ya bayyana garin kwaki a matsayin abincin da ya riƙe shi a lokacin da ya ke makaranta, don haka ya bayyana cewa bai san lokacin da zai daina shan garin ba duk da cewa ya zama gwamna a yanzu.
Ododo ya bayyana haka ne cikin wani gajeren bidiyon da aka ɗaukeshi a lokacin da ya ke shan gari cikin dare, inda wanda ya dauki bidiyon ya yi barazanar yaɗawa amma gwamnan ya ce ko a jikinsa.
Gwamnan ya ce gari ya riga da ya bi jikinsa, don haka a duk lokacin da ya ke shan gari ya na tuna rayuwar da ya yi a makaranta ne a lokacin da ya ke karatu.
“Gari ya riga da ya bi jikina, kuma zan ci gaba da sha domin shi ya riƙeni a lokacin da na ke makaranta”. In ji gwamnan.