
Rahotanni sun bayyana cewa, a yanzu tukunyar shinkafa dafa duka wadda mutane 5 zasu iya ci a gida sai an kashe mata Naira 25,486 kamin ta bada abinda ake so.
Hakan ya nuna an samu karin kaso 20 cikin 100 na farashin dafa shinkafar idan aka kwatanta da farashin dafata a watan Sarumba na shekarar 2024 wanda a wancan lokacin Naira 21,300 ake kashewa wajan Dafa shinkafar.
SBM na fitar da bayanai akai-akai kan farashin dahuwar shinkafa kasancewarta itace abu mafi saukin sarrafawa a gidajen ‘yan Najeriya.
Kuma wannan farashi da suka bayyana suna maganar shinkafa ce wadda ta ji komai tun daga nama mai Albasa da komai dai da ake hadawa shinkafa dafa duka irin su kayan miya magi da sauransu.
Sun alakanta hauhawar farashin da tashin farashin kayan masarufi wanda hauhawar farashin man fetur da rashin tsaro suka jawo.