Monday, December 16
Shadow

Tsananin Rashin Tausayi: An Sace Wata Mata Mai Juna Biyu A Hanyar Zuwa Asibiti

Rahotanni sun bayyana cewa an sace wata mata mai juna biyu mai suna Mrs Ogunbunmi a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.

Majiyar mu ta rawaito cewa Matar wadda aka ce za ta haihu ta bar gidanta da ke Oke Lantoro zuwa babban asibitin jihar, Ijaiye dake Abeokuta,sai dai an yi garkuwa da ita a hanya.

Mijinta, Ogunbunmi Lateef, ya ce ya samu sakon WhatsApp da ke sanar da shi sace matarsa.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, Omolola Odutola, ya tabbatar da faruwar lamarin amma bai yi cikakken bayani ba.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, a ranar Alhamis, ta ce, “Wani Ogunbunmi Lateef na Oke Lantoro ya rawaito cewa matarsa mai juna biyu da za ta haihu ta bar gida zuwa Asibitin Jihar Ijaiye Abeokuta.

Karanta Wannan  'Ɗaliban Najeriya sama da miliyan tara ne suka nemi bashin karatu'

Ogun na daya daga cikin jihar da ke fama da yawaitar laifuka a yankin Kudumaso Yamma.

Daga: Abbas Yakubu Yaura

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *