
Tsohon shugaban sojojin Najeriya, Janar Tukur Yusuf Buratai ya bayyana cewa, Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta jefa ‘yan Najeriya cikin matsin talauci.
Ya bayyana hakane a wajan taron zagayowar ranar haihuwar tsohon Ministan sufuri, Rotimi Amaechi.
Yace gwamnatocin baya a hankali suka rika jefa ‘yan Najeriya cikin talauci amma Gwamnatin Tinubu, Lokaci guda ta jefa mutane saboda tsare-tsaren ta data gudanar masu tsauri.
Saidai yayi fatan nan da shekaru biyu masu zuwa a samu saukin rayuwa wanda yace idan ba haka ba, akwai matsala.