
Jama’a da yawa a kafafen sada zumunta sai yabon Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai suke yi saboda irin kulawar da ya baiwa mahaifiyarsa lokacin tana raye.
Ko da yana Gwamna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya rika baiwa Mahaifiyarsa Lokaci sosai yana bata kulawa.
Wani Bidiyo da aka gani na mahaifiyar Nasiru tana yaba masa tana masa kirari ya karade kafafen sada zumunta sosai.