
Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya bayar da labarin yanda ta kaya a shekarar 2015 da ya nemi sake cin zabe a karo na biyu.
Ya bayyana hakane a yayin da ya je bikin cikar Chief Mike Aiyegbeni Oghiadomhe shekaru 50 da haihuwa.
Yace yawanci ‘yan siyasa sun yaudareshi ne a 2015, yace siyasar Najeriya akwai cin amana sosai a cikinta, yace da wuya ka samu wanda zai tsaya kan magana daya ta gaskiya.
Yace amma Chief Mike Aiyegbeni Oghiadomhe mutum ne me nagarta wanda yana sonshi da gaske.