Friday, December 26
Shadow

Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana abinda za’a yi dan girmama Fafaroma da ya mùtù

Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya mika sakon ta’aziyyarsa ga kiristoci kan mutuwar fafaroma.

Ya bayyana cewa fafaroma mutum ne da ya nuna tausai ga talakawa da ‘yan Cirani da sauransu.

Ya bayyana cewa, sakon karshe na Fafaroma shine kiran da yayi a kawo karshen yakin Gaza.

Dan hakane ma Buhari a sakon da ya fitar ta hannun kakakinsa, Malam Garba Shehu yayi kira ga kasar Israela da kungiyar Hamas da su kawo karshen yakin a matsayin girmamawa ga Fafaroman.

Karanta Wannan  Da Duminsa: Jam'iyyar ADC ta su Atiku ta sanar da sabon gurin taro bayan da Otal da suka yi shirin yin taron a cikinsa yace taron bazai yiyu ba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *