Friday, December 26
Shadow

Usman da Umar (AS) zasu iya canja hukuncin da Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) yayi kuma hakan yayi daidai>>Inji Sheikh Dr. Ahmad Gumi

Babba Malamin Addinin Islama, Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya bayyana cewa, Sahabban Annabi(Sallallahu Alaihi Wa Sallam) Umar da Usman (AS) zasu iya canja hukuncin sa Annabi(Sallallahu Alaihi Wa Sallam) yayi kuma hakan yayi daidai.

Yace Annabi(Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ya basu wannan matsayi na cewa, duk hukuncin da suka yi ya zama shari’a.

Malam ya bayyana hakane a wajan karatun da yake ranar Juma’a a masallacin Sultan Bello dake Kaduna a ranar 22/8/2025.

Wakilin hutudole ya halarci wajan karatun inda malam yayi wannan maganane a yayin da yake bayar da misalin ikirarin ‘yan shi’a na cewa, Khalifanci Aliyu (AS) ne ya kamata a baiwa kuma Annabi(Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ya bar wasiyya kan hakan.

Karanta Wannan  APC ta lashe duka ƙananan hukumomi 13 a zaɓen jihar Nasarawa

Malam yace ko da ace Annabi(Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ya bar wasiyya akan hakan amma sai Umar da Usman suka zabi Abubakar to hakan yayi daidai.

Malam ya kawo misali da cewa, a lokacin da zafin ciwon ajali ya dabaibaye Annabi(Sallallahu Alaihi Wa Sallam) yace a kawo ya rubutawa mutane abinda idan suka bishi ba zasu bata ba.

Malam yace Umar ne ya hana, saboda yayi tunanin cewa Ga wahayin Qur’ani da Hadisai duk basu isa shiriya ba, sai yanzu ne za’a ce a bayar da shiriya? Yace kuma haka aka yi.

Malam Yace bayan Annabi(Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ya farfado bai sake yin maganar ba.

Karanta Wannan  Da Duminsa: 'Yan Bìndìgà sun tare 'yansandan Najeriya sun kashe 2 daga ciki

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *