
Tsohon dan takarar shugaban kasa, kuma mawallafin jaridar Sahara Reporters, Omoyele Sowore ya bayyana cewa, Jahilan Gwamnonin da suka bayar da hutun makaranta saboda zuwan watan Ramadan ‘ya’yansu basa zuwa wadannan makarantun Gwamnatin da suka kulle.
Ya kara da cewa, sun kai ‘ya’yansu can makarantun kudi a Abuja ko kuma kasashen waje.
Sowore ya bayyana hakane a shafinsa na sada zumuntar Facebook.
A baya ma dai Sowore ya kira Gwamnonin jihohin Kebbi, da Kano, da Bauchi da Katsina da cewa Jahilaine saboda sun kulle makarantu saboda zuwan watan Ramadan.
Inda yace idan ya zama shugaban kasa, ba zai yadda a rika kulle makarantun ba.
Lamarin kulle makarantun dai ya jawo cece-kuce sosai inda cikin wadanda suka soki hakan hadda kungiyar Kiristoci ta CAN, da Ministar Ilimi, Suwaiba Ahmad.