
Kakakin majalisar dattijai, Sanata Godswill Akpabio ya bayyana cewa, Majalisar mata ta majalisar Dinkin Duniya da Sanata Natasha Akpoti ta kaishi kara bata da hurumin da zata iya kiransa ya gurfana a gabanta.
Ya bayyana hakanne ta bakin me magana da yawunsa, Eseme Eyiboh inda ya kara da cewa, lamarin na cikin gidane dan haka babu wanda ya isa ya saka musu baki.
Yace majalisar bata da hurumin a matsayin Najeriya ta kasa me cin gashin kanta tace zata shiga wannan lamari.
Saidai yace babban abin jin ma shine, sanata Natasha Akpoti tace ta kai magana kotu, shin me ya kaita rugawa majalisar Dinkin Duniya kuma tace can ma ta kai kara? Yace hakan sabawa doka ne.
Yace amma tunda magana na kotu, ba zai so yayi ta surutu akai ba.
Saidai yace wannan abu da sanata Natasha Akpoti ta yi kawai ta yi shine dan ta kunyata Najeriya.
Da aka tambayeshi shin ko wannan abu da sanata Sanata Natasha Akpoti ta yi zai iya sawa a kara dakatar da ita? Sai yace ba zai ce komai game da hakan ba.