Rahotanni sun bayyana cewa, wahalar rayuwa a Najeriya tasa mata sun fara aikin jari Bola wanda aiki ne da aka fi sanin maza da yi.
An ga matan na aikin Jari Bola ne a Jihar Legas inda jaridar Vanguard tace yawancinsu matan aurene.
Wasu daga cikin matan da jaridar ta yi hira dasu sun bayyana cewa, Mazajensu ne suka rasu wasu kuma sun bayyana cewa an kori mazajensu daga wajan aiki ne da dai sauran matsalolin rayuwa.
Tun bayan hawan mulkin Shugaba Bola Ahmad Tinubu kuma ya cire tallafin man fetur a ranar farko da ya karbi mulkin, kasar ta fada cikin matsin tattalin arziki wanda har yanzu ba’a warware ba.