
Hukumar sojojin Najeriya tace zata bi sahun wadanda suka kai hari a jihar Benue suka kashe mutane akalla 100.
Rundunar sojin Najeriya me suna Operation WHIRL STROKE (OPWS) karkashin jagorancin Major General Moses Gara ta kai ziyara jihar ta Benue ranar Asabar, June 14, 2025.
Kakakin rundunar, Lieutenant Ahmad Zubairu Zubairu ya bayyana cewa sun kai ziyarar ne a kokarin mayar da martani da suke ga harin da ya faru.
A yayin ganawa da jama’ar garin, Major General Moses Gara ya bayyana cewa, harin yayi muni kuma zasu bi sahun wadanda suka kaishi dan ba za’a amince da hakan ba.