
Shahararren dan fim din Yarbawa, Ganiu Nafiu ya bayyana cewa, yayi danasanin goyon bayan shugabab kasa, Bola Ahmad Tinubu a zaben 2023.
Dan fim din wanda aka fi sani da sunan Alapini ya bayyana cewa sun shafe watanni 2 suna yiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yakin neman zabe amma tun da ya zama shugaban kasar bai kara kallonsu ba.
Yace shi da ‘yan fim din da yawa suna dana sanin goyon bayan da suka baiwa shugaban kasar.