
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa an gaya masa shine zai ci zaben shekarar 2027.
Ya bayyana hakane a yayin da ya je addu’ar 7 ta marigayin basaraken jihar Ogun, Awujale, Oba Sikiru Adetona.
Shugaba Tinubu yace a yayin da yake yakin neman zaben shugaban kasa a 2022, ya kaiwa basaraken ziyara inda ya saka masa albarka sannan ya gaya mai cewa shine zai yi nasara a zaben.
Sannan yace ya kuma kara gaya mai cewa shine dai zai sake lashe zaben shekarar 2027.
Shugaba Tinubu yace amma yanzu gashi ya tafi ya barmu a Duniya.