Tuesday, September 15
Shadow

Wanda ya gayamin nine zanci zabe a 2023 ya sake gayamin nine zan ci zaben 2027>>Inji Shugaba Tinubu

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa an gaya masa shine zai ci zaben shekarar 2027.

Ya bayyana hakane a yayin da ya je addu’ar 7 ta marigayin basaraken jihar Ogun, Awujale, Oba Sikiru Adetona.

Shugaba Tinubu yace a yayin da yake yakin neman zaben shugaban kasa a 2022, ya kaiwa basaraken ziyara inda ya saka masa albarka sannan ya gaya mai cewa shine zai yi nasara a zaben.

Sannan yace ya kuma kara gaya mai cewa shine dai zai sake lashe zaben shekarar 2027.

Shugaba Tinubu yace amma yanzu gashi ya tafi ya barmu a Duniya.

Karanta Wannan  'Yan majalisar Tarayya sun nemi Kotu ta tursasa Gwamnonin PDP su biyasu Naira Biliyan 1 saboda gwamnonin sun shigar da karan neman Shugaba Tinubu ya janye dakatarwar da yawa Gwamnan jihar Rivers, Simi Fubara

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *